Myanmar

Dubban ma'aikata a Myanmar sun shiga yajin aiki domin kwatar 'yanci

Masu zanga-zangar adawa da juyin mulkin sojoji a Myanmar.
Masu zanga-zangar adawa da juyin mulkin sojoji a Myanmar. AP

Dubban mai’aikata a Myanmar na cigaba da yajin aikin da ya shafe watanni fiye da biyu yana gudana, matakin da suke fatan zai tilastawa sojojin da suka hambarar da gwamnatin Aung San Su Kyii su mikawa farar hula mulki.

Talla

Daga cikin dubban mutanen dake yajin aikin a Myanmar akwai Likitoci, ma’aikatan banki, injiniyoyi, jami’an kwastam da kuma ma’aikatan masana’antu, wadanda wasaunsu ke cikin akalla mutane 550 da suka rasa rayukansu, yayin arrangama tsakaninsu da jami’an tsaro a zanga-zangar da suka watanni fiye da biyu suna y ikan adawa da juyin mulkin sojojin kasar.

Rahotanni sun ce tuni matakin ta soma tasiri kan tattalin arzikin kasar ta Myanmar mai fama da masassara ba ya ga ta tasirin annobar Korona.

Ma’aikatan na Myanmar sun ce zabin shiga yajin aikin. don gurgunta tattalin arzikin nasu, ya zame musu dole ne, saboda fargabar fuskantar kisan gilla, idan suka fita zanga-zanga.

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.