China - Faransa

Kungiyoyi sun hukunta masaku masu ci da gumin 'yan Kabilar Uyghur

Wasu 'yan Kabilar Uyghur yayin zanga-zangar a birnin Brussels, domin nemawa 'yan uwansu 'yanci daga gwamnatin kasar China.
Wasu 'yan Kabilar Uyghur yayin zanga-zangar a birnin Brussels, domin nemawa 'yan uwansu 'yanci daga gwamnatin kasar China. AP - Francisco Seco

Wata gamayyar kungiyoyin fararen hula a Faransa ta bukaci gwamnatin kasar da ta gudanar bincike kan wasu manyan kamfanonin samar da kayayyaki dake kasar, bisa zarginsu da samun riba daga bautar da ‘yan kabilar Uyghur na kasar China, da ake azabtarwa.

Talla

Kamfanonin sana’anta kayayyakin sawar da korafin kungiyoyin fararen hular ya shafa a Faransa sun hada da Inditex, Uniqlo, SMCP da kuma Skechers mai sana’anta takalma.

Kungiyoyin fafutukar dai na tuhumar wadannan kamfanoni da boye bayanan yadda ake bautar da ‘yan kabilar ta Uyghur dake China ta hanyoyin tilasta musu noma da ayyukan wahala kan noman audugar da masana’antun ke bukata, baya ga cin zarafinsu da ake yi, a sansanonin da ake tsare da su a yankin Xinjiang.

Kungiyoyin fararen hular da suka rubuta takardar koken sun hada da Sherpa dake fafutukar kare hakkokin walwalar ma’aikatan kamfanonin sana’anta kayayyaki da cibiyar masu rajin kare hakkin ‘yan Uyghur dake Turai, sai kuma wata mata daya daga cikin ‘yan kabilar da ta tsira daga China.

Kungiyoyin kare hakkin dan adam sun kiyasta cewar ‘yan kabilar Uyghur akalla miliyan 1 ne tare da wasu kabilun da mafi akasarinsu Musulmi ne hukumomin China suka killace cikin sansanoni a yankin Xinjiang, inda ake zargin ana bautar dasu tare da azabtarwa, sai dai Chinar na cigaba da musanta zarge-zargen.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.