Iran - Nukiliya

Iran ta ci gaba da shirinta na sarrafa makamashin Uranium

Shugaban Iran Hassan Rouhani yayin kaddamar da shirin sake ci gaba da sarrafa mukamishin Uranium a daya daga cikin cibiyoyin da ke kasar, 10 ga watan Afrelu 2021
Shugaban Iran Hassan Rouhani yayin kaddamar da shirin sake ci gaba da sarrafa mukamishin Uranium a daya daga cikin cibiyoyin da ke kasar, 10 ga watan Afrelu 2021 © AFP / Iranian Presidency

 Iran ta sanar da ci gaban shirinta na inganta makamashin Uranium a wani matakin da ya saba wa yarjejeniyar nukiliya ta shekarar 2015 da ke cikin rudani, kwanaki bayan da aka fara aka tattaunawa kan ceto yarjejeniyar.

Talla

Shugaba Hassan Rouhani a hukumance ya kaddamar da Shirin a wani biki da aka watsa kai tsaye da gidan talabijin din kasar.

Daya daga cibiyoyin sarrafa mukamashin Uranium na Iran, wanda ta fara aikin ci gaba da aiki. 10 ga watan Afrelu 2021.
Daya daga cibiyoyin sarrafa mukamashin Uranium na Iran, wanda ta fara aikin ci gaba da aiki. 10 ga watan Afrelu 2021. HO Atomic Energy Organization of Iran/AFP/File

Matakin na baya-bayan nan da Iran ta dauka na kara inganta uranium ya biyo bayan bude zagayen tattaunawar ranar Talata tare da wakilan sauran bangarorin da suka rage a yarjejeniyar nukiliyar kan dawo da Amurka cikin ta.

Tsohon shugaban Amurka Donald Trump ya fice daga yarjejeniyar a shekarar 2018.

Iran dai ta bukaci janye takunkuman da tsohon shugaban Amurka Donald Trump ya kakkaba mata a shekarar 2018, domin komawa mutunta yarjejeniyar nukiliyar ta.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.