China

China na kokarin ceto ma'aikatan da suka makale karkashin kasa

Masu aikin ceto a kasar China lokacin da suke aikin kubutar da ma'aikatan hakar ma'adanai da suka makale a karkashin kasa, 22 ga watan Janairun shekarar 2021
Masu aikin ceto a kasar China lokacin da suke aikin kubutar da ma'aikatan hakar ma'adanai da suka makale a karkashin kasa, 22 ga watan Janairun shekarar 2021 REUTERS - ALY SONG

Masu aikin ceto a kasar China na can suna kokarin kubutar da wasu ma'aikatan 21 da suka makale a wata mahakar kwal a yankin Xinjiang da ke arewa maso yammacin kasar, bayan ambaliyar da ta yanke wutar lantarki a karkashin kasa tare da katse hanyoyin sadarwa.

Talla

Hatsarin ya faru ne a mahakar kwal ta Fengyuan da ke gundumar Hutubi a yammacin ranar Asabar, lokacin da ma'aikata ke gudanar da ayyukan inganta aikin a wurin, acewar kamfanin dillacin labarai na Xinhua.

Rahotanni sunce, an samu nasarar kubutar da takwas daga cikin ma’aikata 29 da ke mahakar.

A watan Janairu, ma’aikata 22 sun makale a wata mahakar ma’adinai a lardin Shandong da ke gabashin China bayan fashewar wani abu ya lalata hanyar shiga, lamarin da ya sa ma’aikatan suka makale a karkashin kasa na kimanin makonni biyu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.