Pakistan-Faransa

Faransa ta bukaci al'ummarta su gaggauta barin Pakistan saboda rikici

zanga-zangar kin jinin Faransa da Faransawa a birnin Islamabad na Pakistan.
zanga-zangar kin jinin Faransa da Faransawa a birnin Islamabad na Pakistan. AP Photo/A.H. Chaudary

Ofishin jakadancin Faransa a birnin Islamabad ya umarci daukacin Faransawa su gaggauta barin Pakistan bayan tsanantar zanga-zangar kin jinin Faransa da ke kokarin kassara al’amura a wannan makon don nuna bacin rai game da zanen batanci da aka yiwa fiyayyen halitta.

Talla

A wani sako da Ofishin jakadancin na Faransa da ke Islamabad ya aikewa daukacin Faransawa da ke sassan Pakistan ya ce sakamako barazanar da ke tsananta ga kadarorin Faransa da al’ummarta a cikin kasar ya zama wajibi su gaggauta ficewa na dan wani lokaci gabanin daidaituwar al’amura.

Ofishin jakadancin ya ce Faransawan da ma’aikatan kamfanoninsu da ke cikin kasar su yi amfani da jiragen kasuwancin da suke aiki yanzu haka wajen barin kasar cikin gaggawa.

Watanni kenan Pakistan na fuskantar zanga-zangar kin jinin Faransa tun bayan zanen batancin da mujallar barkwanci ta Charlie Hebdo ta yi ga fiyayyen halitta, lamarin da ke matsayin babban zunubi a tanadin addinin Islama.

Sai dai a baya-bayan nan ne zanga-zangar ta fara juyewa zuwa rikici, bayan da jagoran jam’iyyar Tehreek-e-Labbaik Pakistan Saad Rizvi ya bukaci korar jakadan Faransa a kasar, wanda ya kai ga kame shugaban bayan tsanantar rikicin.

Zuwa yanzu jami’an ‘yansanda biyu suka rasa rayukansu a tarzomar yayinda wasu da dama suka jikkata.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.