Pakistan

A hukunta masu cin zarafin Islama daidai da masu musanta kisan Yahudawa - Khan

Franministan Pakistan Imran Khan, yayin wata ziyara a Putrajaya, na Malaisiya ranar 4 ga watan Fabrairun 2020.
Franministan Pakistan Imran Khan, yayin wata ziyara a Putrajaya, na Malaisiya ranar 4 ga watan Fabrairun 2020. REUTERS/Lim Huey Teng

Firaministan Pakistan Imran Khan ya bukaci gwamnatocin kasashen Yammacin duniya da su rika daukar duk mutumin da ya zagi Annabi Muhammadu mai tsira da amincin Allah su tattabata a gareshi, tamkar wadanda suke musanta kisan kiyashin yahudawa.

Talla

Da yake jawabi bayan kwashe mako guda ana mummunar zanga-zanga a Pakistan wanda wata kungiyar masu tsattsauran ra'ayin Islama ta jagoranta domin nuna fushinta kan goyon bayan gwamnatin Faransa ga mujallar kasar da ta wallafa zane-zanen batanci ga manzon tsiri annabi Mohammad, (SAW).

Khan ya ce zagin annabin na cutar da Musulmi a fadin duniya.

"Mu Musulmai muna da matukar kauna da girmamawa ga Annabinmu," kamar yadda ya wallafa a shafinsa na Twitter.

A hukunta masu cin zarafin Isalama daidai da masu musanta kisan Yahudawa - Khan

 

"Ba za mu iya jure wa irin wannan rashin mutunci da cin zarafi ba."

 

Tuni mahukutar kasar suka haramta kungiyar TLP da ta jagoranci zanga-zangar da yayi sanadiyar mutuwar  ‘yan sanda hudu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.