Iran - Nukiliya

Iran ta bukaci tsare mutumin da ya kai hari cibiyar Nukiliyarta

Shugaban hukumar mukamashi na kasar Iran Ali Akbar Salehi lokacin da yake magana da shugaban kasar Hassan Rouhani cikin cibiyar Nukilyar kasar ranar 9 ga watan Afrelun shekarar 2019.
Shugaban hukumar mukamashi na kasar Iran Ali Akbar Salehi lokacin da yake magana da shugaban kasar Hassan Rouhani cikin cibiyar Nukilyar kasar ranar 9 ga watan Afrelun shekarar 2019. HO Iranian Presidency/AFP/File

Iran ta gabatar da sunan mutumin da take so a kama shi dangane da alakarsa da fashewar da ya auku a tashar Nukiliyarta dake Natanz, wanda ya haddasa daukewar wutan lantarki kwanakin baya, yayin da tattaunawa ke gudana a Vienna a kokarin ceto yarjejeniyar nukiliyar Tehran na shekarar 2015 da manyan kasashen duniya.

Talla

Gidan talabijin din kasar ya ruwaito Ma'aikatar leken asirin Iran ta bankado "Reza Karimi, amatsayin wanda ya kisa wannan aika-aika.

Sanarwar tace, wanda ake zargin ya gudu daga Iran kafin fashewar ranar Lahadin da ta gabata da kasar ta zargi Isra’ila da alhaki.

Jami'an kasashen da suka rage a yarjejeniyar nukiliyar Iran sun fara wani taro a hukumance a Vienna, suna masu cewa wannan zagayen tattaunawar da aka fara a ranar Alhamis zai kawo karshen matsalar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.