Pakistan-Faransa

Imran Khan ya roki al'ummar Pakistan su kawo karshen zanga-zanga

Firaministan Pakistan Imran Khan.
Firaministan Pakistan Imran Khan. Wakil KOHSAR AFP/File

Firaministan Pakistan Imran Khan ya roki kungiyar Tahreek-e- Labbaik Pakistan da ke zanga zangar adawa da kasar Faransa da ta dakatar da bukatar ta na ganin Jakadan kasar ya bar Pakistan, inda ya ke cewa matakin na batawa kasar su suna.

Talla

Tun makon jiya yayan wannan kungiyar suka kaddamar da zanga zanga bayan tsare shugaban su saboda kiran da yayi suyi tattaki zuwa babban birnin kasar domin korar Jakadan Faransa.

Kungiyar ta kaddamar da kamfe na yaki da manufofin Faransa tun bayan da shugaba Emmanuel Macron ya kare Mujallar Charlie Hebdo da ta wallafa zaben fiyayyen halitta Annabi Muhammad tsira da amincin Allah su kara tabbata a gare shi.

Firaministan ya ce ya na bukatar hana batanci ga Annabin rahma da sunan 'yanci amma kuma ba zai iya korar jakadu a ko da yaushe ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.