Saudi-Iran

Mu na maraba da duk wata tattaunawa tsakaninmu da Saudiya- Iran

Tawagar wasu daga cikin shugabannin Gabas ta tsakiya da suka kunshi wakilcin Saudiya da na Iran.
Tawagar wasu daga cikin shugabannin Gabas ta tsakiya da suka kunshi wakilcin Saudiya da na Iran. REUTERS/Faisal Al Nasser

Ma'aikatar harkokin wajen Iran ta ce kasar a shirye ta ke kuma tana maraba da duk wata tattaunawa tsakaninta da Saudiya, duk da tsamin alakar da ke tsakaninsu kusan shekaru 6 da ya kai ga yanke hulda.

Talla

Kakakin ma'aikatar Saeed Khatibzadeh yayin zantawarsa da jaridar Financial Times ya ce a kowanne lokaci Iran na farin cikin tattaunawa da Saudi Arabia, dai dai lokacin da jita-jitar ganawa tsakanin wakilan bangarorin biyu ke ci gaba da karade kafofin yada labarai.

Sai dai Saeed Khatibzadeh ya ki amsa tambayar gaskiyar batun ganawar bangarorin biyu a Iraqi da nufin gyara alakar da ke tsakanin kasashen biyu wadda ta wargaje tun a 2016, inda ya ce ita kanta Iran ta samu labarin ne a jaridun Duniya.

Kasashen biyu dai na banbancin akida a muhimman al'amuran da suka shafi gabas ta tsakiya ciki har da rikicin kasar Yemen inda Iran ke goyon bayan 'yan tawaye a bangare guda Saudiya ke goyon bayan gwamnatin hadin kan kasar.

A cewar Khatibzadeh Iran na goyon bayan tattaunawa tsakaninta da babbar abokiyar gabar ta ta Saudiya la'akari da yadda sulhu tsakaninsu zai amfani al'ummomin kasashen biyu haka zalika zai daidaita al'amura a gabas ta tsakiya.

Wasu majiyoyi sun bayyana cewa kasashen biyu sun faro tattaunawa a Iraqi ne kan batun yakin kasar Yemen wanda kuma bayanai ke cewa da yiwuwar samun nasara. 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.