Indonessia

Indonessia ta baza jiragen yaki don nemo jirgin ruwanta da ya bace

Jiragen ruwan yakin Indonessia
Jiragen ruwan yakin Indonessia via REUTERS - ANTARA FOTO

Jiragen ruwan yakin kasar Indonesia 6 sun fara shawagin neman wani jirgin ruwa mallakin kasar da ya bace dauke da fasinjoji 53, da kuma jirage masu saukar angulu a mashigin ruwar kasar.

Talla

A cewar hukumomin kasar, babban abin tashin hankalin shine yadda mutanen cikin jirgin ke da karancin Iskar Oxygen da rashin ta zai iya hallaka su cikin gaggawa.

Haka kuma an ga nason mai a dai-dai gurin da ake zargin jirgin ya nutse, al’amarin da ya sanya hukumomin kasar suka hakikance cewa tankin man jirgin ne ya fashe.

Dole a gano jirgin da ya bace

Shugaban hukumar kula sufurin jiragen ruwan kasar Yudo Margono ya ce ya zama wajibi a yi duk mai yiwuwa wajen gano jirgin kafin nan da jibi Asabar, matukar ba haka ba kuwa tabbas akwai fargabar a samu tashin hankali a kasar.

Sai dai kuma tuni kwararru kan tsaron kasar ta ruwa suka ce akwai yiwuwar tuni mutanen jirgin ma sun hallaka, don kuwa zurfin ruwan da ke da nisan kilomita dari bakwai wato taku dubu 2 da dari 3 ka iya dagargaza jirgin kan ya kai kasa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.