India - Coronavirus

Kusan mutane dubu 400 suka harbu da korona a India cikin kwana daya

Jami'an kiwon lafiya dake kula da masu dauke da cutar korona a kasar India
Jami'an kiwon lafiya dake kula da masu dauke da cutar korona a kasar India REUTERS - ADNAN ABIDI

Gwamnatin India ta bayyana samun mutanen da suka harbu da cutar korona yau asabar da yawan su ya kai dubu 346,786 wanda shine mafi yawa da duniya ta gani tun bayan barkewar cutar a watan Disambar shekarar 2019.

Talla

Alkaluman da hukumomin lafiyar kasar suka gabatar ya nuna cewar ayau asabar an samu mutane dubu 346,786 da suka harbu da cutar sabanin dubu 332,730 da aka gani jiya juma’a.

A jiya juma’a mutane dubu 893,000 suka harbu da cutar a fadin duniya, kuma kashi daya bisa uku daga cikin su sun fito ne daga kasar India.

Hukumomin India sun ce mutane 2,624 suka mutu ayau asabar, abinda ya kawo adadin mutanen da cutar ta kashe a kasar zuwa kusan 190,000.

Asibitocin sun cika kuma ana bukatan Oxygen

Yanzu haka asibitocin kasar sun cika da marasa lafiya, yayin da ake fama da karancin iskar taimakawa marasa lafiyar numfashi.

Hukumomin kasar sun nemi a taimaka musu da iskar ta Oxygen kuma tuni wasu kasashe suka bayyana aniyar taimaka musu ciki harda Birtaniya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.