India-Coronavirus

Tsanantar Covid-19 a India ya zarta yadda ake tunani- WHO

Yadda ake kone gawarwakin mutanen da corona ta kashe gab da asibitocin da suka mutu.
Yadda ake kone gawarwakin mutanen da corona ta kashe gab da asibitocin da suka mutu. REUTERS - ADNAN ABIDI

Hukumar Lafiya ta Duniya WHO ta koka kan halin da ake ciki a India inda ta ce yanayin ya wuce yadda ake tunani bayan tsanantar mace mace dama karuwar sabbin kamuwa da cutar ta Covid-19 wadda ke kashe kusan mutum dubu 3 kowacce rana.

Talla

Shugaban hukumar Lafiya ta Duniya WHO Tedros Adhanom Ghebreyesus ya bayyana halin da ake ciki a India yanzu haka a matsayin mai karya zuciya, yana mai cewa hukumar a shirye ta ke ta gaggauta taimakawa kasar ta kowacce fuska.

Tsanantar cutar ta Coronavirus ya tilasta sake sanya dokar kulle a sassan kasar musamman birnin New Delhi inda cutar ta tsananta matuka, bayan yankewar iskar taimakawa masu cutar da ke fama da sarkewar lumfashi a sassan kasar baki daya.

Tuni dai WHO ta bi sahun manyan kasashen wajen tallafawa India da kayakin ceto rayukan masu cutar wadanda ke ci gaba da mutuwa sakamakon karancin kayakin bayar da kariya da kuma yankewar magunguna da kuma karancin gadaje a asibitoci.

A cewar Tedros Adhanom yanzu haka kwararrun jami’an hukumar fiye da dubu 2 da 600 sun isa kasar ta India don bayar da agajin daya kamata sakamakon tsanantar cutar.

India wadda zuwa yanzu al’ummarta dubu 195 suka mutu sanadiyyar cutar, a jiya litinin kadai ta samu sabbin kamuwa dubu 352 da 991 yayinda wasu dubu 2 da 812 suka mace adadi mafi yawa da kasar ta gani a rana guda.

Al’ummar kasar ta India mai yawan mutane fiye da biliyan 1 da miliyan 300 na amfani da kafofin sada zumunta wajen neman dauki ga marasa lafiyan na su dama bayyana halin da kasar ke ciki a yaki da cutar ta Covid-19.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.