Isra'ila

Mutane 44 sun mutu a turmutsitsin wajen ibadar Yahudawa

Taron Yahudawa a birnin Jerusalem.
Taron Yahudawa a birnin Jerusalem. AHMAD GHARABLI AFP

Mummunan turmutsitsin a  wurin ibadar Yahudawa da ya cika makil da mutane ya kashe a kalla yahudawa 44 a arewacin Isra’ila, yayin da masu aikin ceto ke fuskantar matsalolin agaji sakamakon cunkoson jama’a a kokarinsu na kwashe wadanda suka jikkata.

Talla

Iftila’in ya auku ne a Meron, wani wuri mai tsarki ga yahudawa da ke tururuwa duk shekara don yin bikin Lag BaOmer.

Firminista Benjamin Netanyahu, wanda aka kai shi wurin da lamarin ya auko a cikin jirgi mai saukar ungulu ya walafa a shafinsa na Twitter cewa ‘iftil’in tsaunin Meron’ yana daya daga cikin munanan bala’o’in da suka afka wa kasar tun da aka kafa ta shekaru 70 da suka wuce.

An rufe wurin bara saboda dokokin coronavirus, inda aka bude wannan shekara saboda nasararori da kasar ke ganin ta samu wajen aikin allurar rigakafin cutar korona.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.