Japan

Girgizar kasa mai karfin maki 6.8 ta auku a gabar tekun Japan

Wasu da suka rasa gidajensu sakamakon girgizar kasa a kasar Japan
Wasu da suka rasa gidajensu sakamakon girgizar kasa a kasar Japan Reuters / Kyodo

Girgizar kasa mai karfin maki 6.8 ta afku a gabar tekun arewa maso gabashin Japan yau Asabar, to sai dai babu barazanar guguwar tsunami a cewar hukumomi, kuma ba’a bayyana adadin barna da ta tayi ba ya zuwa yanzu.

Talla

Hukumar Kula da Yanayin Kasa ta Amurka ta ce girgizar kasar ta asuba ta afku a zurfin kilomita 47 a cikin tekun Pacific, kusa da Ishinomaki a lardin Miyagi – wanda ya haifar da tsunami a shekarar 2011, da ya hallaka sama da mutane dubu 18.

Hukumar kula da yanayi ta Japan ta ce babu wani hatsarin tsunami da zai biyo bayan iftila’in na yau, duk da girgiza mai karfi da ya haifar a sassan gabashin gabar tekun wanda kuma aka ji ta a Tokyo.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.