India-Coronavirus

Gobara ta kashe masu jinyar korona 12 a kasar India

Yadda ake kona gawakin wadanda cutar korona ta kashe a kasar India
Yadda ake kona gawakin wadanda cutar korona ta kashe a kasar India Gagan NAYAR AFP

Akalla marasa lafiya masu fama da annobar Covid-19 su 12 suka mutu yau Asabar a kasar India sakamakon gobara da ya tashi a sashin asibitin inda ake kulawa da su.

Talla

Kasar India na fama da yawaitan gobara a asibitocin da ake kula da masu dauke da cutar korona, ko a ranar 23 ga watan Afrilu wata gobara a wajen garin Mumbai ta kashe masu dauke da cutar 13 Covid-19, 'yan kwanaki bayan wata gobarar da ta yi sanadin mutuwar mutane 22 a wani asibitin, a jihar Maharashtra.

A watan da ya gabata wasu marasa lafiya 22 masu cutar Coronavirus sun mutu a wani asibiti a cikin wannan jihar lokacin da iskar oxygen ɗin da ke kara musu iska ta katse ta dalilin yoyon da ya yi.

Tsarin kiwon lafiyar Indiya ya dade yana fama da karancin kudi, kuma sabon barkewar cutar ya kara dagula mata al’amura tare da tsananin bukatar iskar oxygen da magunguna da gadajen asibiti, inda marasa lafiya ke mutuwa a wajen asibitoci a wasu yankuna.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI