Afghanistan-Amurka

Harin Taliban ya hallaka musulmai dake bude baki a Afghanistan

Sojojin Amurka da suka fara janyewar karshe a kasar Afghanistan Asabar 1 ga watan Mayu 2021
Sojojin Amurka da suka fara janyewar karshe a kasar Afghanistan Asabar 1 ga watan Mayu 2021 Wakil KOHSAR AFP/File

Akalla mutane 21 suka mutu sannan kusan 100 suka jikkata sakamakon fashewar wata mota dauke da bama-bamai a Afghanistan.

Talla

Shugaban kasar Ashraf Ghani ya zargi Taliban da alhakin Fashewar da ta auku a wani yanki na Pul-e-Alam, babban birnin lardin Logar, yayin da mutane ke buda bakin azumin watan Ramadana.

Mai magana da yawun ma’aikatar cikin gida Tariq Arian ya fadawa manema labarai cewa fashewar ta yi sanadiyar mutuwar mutane 21 tare da jikkata wasu 91, wanda hakan ke sabunta adadin da aka samu a baya.

An kai harin ne gidan saukar baki

Shugaban majalisar lardin Logar, Hasibullah Stanikzai, ya ce bam din da ke cikin motar ya auna wani gidan saukar baki ne a garin da mutane da dama ke zaune - ciki har da daliban jami'a.

Arian ya ce fashewar ta haifar da mummunar barna a yankin, ciki har da asibiti da gidajen zama.

"Rufin gidajen ya ruguje kuma mutane sun makale a karkashin tarkace," in ji shi, ya kara da cewa adadin na iya canzawa. "Jami'an tsaro na kokarin ceto wadanda suka makale."

Janye sojojin Amurka

Wannan na zuwa ne yayin da yau Asabar Sojojin Amurka suka fara janyewar karshe daga Afghanistan, bayan shafe sama da shekaru 20 suna yaki da mayakan Taliban.

Wannan janyewar kawo karshensu a kasar wanda shugaban Amurka Joe Biden ya sanar a tsakiyar watan Afrilu, za a yi shi ne tare da kawancen NATO kuma dole ne a kammala shi a kafin ranar 11 ga watan Satumbar, wanda ke dai-dai da ranar tunawa da harin ta’addancin shekarar 2001 a Amurka.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.