India-Coronavirus

Mutane dubu 400 sun harbu da Korona cikin sa'o'i 24 a India

Ta'azzarar cutar Korona a India, inda a Asabar dinnan hukumomi suka sanar cewa mutane dubu 400 sun harbu cikin sa'o'i 24.
Ta'azzarar cutar Korona a India, inda a Asabar dinnan hukumomi suka sanar cewa mutane dubu 400 sun harbu cikin sa'o'i 24. Prakash SINGH AFP

Annobar coronavirus ta ci gaba da ta’azzara a India a wannan Asabar, inda hukumomi suka sanar da cewa kimanin mutane dubu 400 ne suka harbu da cutar a cikin sa’o’i 24, a yayin da suka ba da damar yi wa kowane baligi rigakakafin cutar duk da karancinsa.

Talla

A halin da ake ciki, hukumomin babban birnin kasar, New Delhi sun tsawaita dokar hana fita da mako guda, a daidai lokacin da kwararren jami’in Amurka kan abin da ya shafi annoba, Anthony Fauci ke cewa kamata ya yi India ta koma kulle na ‘yan makonni.

Watanni 2 da suka wuce, ministan lafiya na India ya ce kasar tana daf da murkushe annobar, inda har take aikewa da rigakafi zuwa kasashen waje, amma  yanzu an dakatar da haka, kuma al’ummar kasar sun kagara a yi musu rigakafi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.