Afghanistan - Taliban

Faɗa tsakanin sojojin Afghanistan da Taliban ya hallaka mutane 100

Cikin wannan hoto da aka dauka 29 ga watan Maris 2012, ana ganin sojojin Jamus dake cikin dakarun kawance dake yaki a Afghanistan na aikin sintiri a yankin Kunduz.
Cikin wannan hoto da aka dauka 29 ga watan Maris 2012, ana ganin sojojin Jamus dake cikin dakarun kawance dake yaki a Afghanistan na aikin sintiri a yankin Kunduz. AFP - JOHANNES EISELE

Gwamnatin Afghanistan tace akalla mutane sama da 100 suka mutu sakamakon arangamar da akayi tsakanin dakarun gwamnati da 'Yan Taliban a cikin sa’oi 24 da suka gabata, a daidai lokacin da sojojin Amurka suka fara janyewa daga kasar.

Talla

Ma’aikatar tsaron Afghanistan tace anyi arangamar tsakanin bangarorin biyu ne a wurare da dama cikin su harda Kandahar inda sojojin Amurka suka kai harin sama ranar Asabar.

Ma’aikatar tace wasu Karin 'Yan Taliban 52 sun samu raunuka, ba tare da Karin bayani akai ba.

Ya zuwa yanzu kungiyar Taliban bata ce komai kan lamarin ba, amma kamfanin dillancin labaran Faransa yace bisa al’ada an san bangarorin biyu da kara yawan mutanen da suka jikkata a lokacin da suka yi arangama da juna.

Arangama tsakanin sojoji da Taliban

A watannin da suka gabata, ana cigaba da samun arangama tsakanin bangarorin biyu ba tare da kaukautawa ba a yakin da aka kwashe shekaru 20 anayi.

Yanzu haka Amurka ta fara janye dakarun ta 2,500 da suka rage a kasar ranar asabar kamar yadda shugaba Joe Biden ya bada umurni.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.