Korea ta Arewa-Amurka

Koriya ta Arewa ta zargi Amurka da yaudara

Shugaban Korea ta Arewa Kim Jung un.
Shugaban Korea ta Arewa Kim Jung un. AP

A yau Lahadi Koriya ta Arewa ta zargi shugaban Amurka Joe Biden da bin manufofin nuna kiyayya, tana mai watsi da abin da ta kira diflomasiyyar yaudara ta Amurka, inda ta yi gargadin mayar da martani a kan duk wani cin zali da za a yi mata.

Talla

A ranar Laraba da ta gabata Biden ya ce gwamnatinsa za ta magance barazanar shirin nuiliyar Koriya ta Arewa ta hanyar diflomasiyya da taka tsantsan.

A ranar Juma’a fadar White House ta ce a shirye shugaba Biden yake don tattaunawa da Koriya ta Arewa a kan batun jingine shirin nukiliyarta, biyo bayan kammala nazarin manufofi, amma Pyongyang ta mayar da martani tana cewa,   Biden ya tafka babban kuskure.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.