Afghanistan-Ta'addanci

Adadin wadanda suka mutu a fashewar Afghanistan ya kai 50

Wasu mutane a afghanistan da ke kokarin gano 'yan uwansu da fashewa ta rutsa da su a kusa da wata makarantar mata a yammacin birnin Kabul.
Wasu mutane a afghanistan da ke kokarin gano 'yan uwansu da fashewa ta rutsa da su a kusa da wata makarantar mata a yammacin birnin Kabul. © AP - Rahmat Gul

Hukumomin Afghanistan sun ce adadin wadanda  suka mutu, yayin sakamakon fashewar wani bam kusa da wata makarantar mata dake yammacin Kabul ya kai 50, da dama kuma sun jikkata, a yayin da kungiyar Taliban ke ci gaba da musanta hannu a aika aikar.

Talla

Mai Magana da yawun ma’aikatar cikin gidan kasar Tareq Arian ya tabbatar da adadin sakamakon hadarin da aka samu a yankin Dasht-e-Barchi, unguwar mabiya Shia, yayin sayayyar bukukuwan salla karama.

A yau Lahadi mutane da dama ke binne ‘yan uwansu da lamarin ya rutsa da su a wani wuri da ake wa lakabi da ‘makarbarta masu shahadu’

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.