China-Kumbo

Kumbon da China ta harba sararin samaniya ya rikito

Wani sashe na kumbon China mai suna Long March-5B rocket, ya rikito a tekun India.
Wani sashe na kumbon China mai suna Long March-5B rocket, ya rikito a tekun India. STR AFP/File

Wani makeken sashe na baraguzan wani kumbon da China ta harba sararin samaniya ya rikito cikin wannan duniya tamu, kana ya tarwatse a tekun Indiya a yau Lahadi, kamar yadda hukumar binciken sararin samaniyar Chinar ta bayyana, biyo bayan rade-radi a kan inda wannan abu mai nauyin tan 18 zai fado.

Talla

Tun da farko sai da hukumomin kasar suka ce babu wani hatsari a tattare da rikitowar wani sashe na baraguzan wannan kumbon da aka wa lakabi da Long March- 5B da ta harba a ranar 29 ga watan Afrilu.

Sun kara da cewa akasarin baraguzan sun tarwatse, kuma sun lalace a yayin rikitowar.

Wannan al’amari ya yi daidai da hasashen kwararru da suka ce dukkanin baraguzan wannan kumbon za su fada teku ne, duba da cewa kashi 70 na duniya yana mamaye ne da ruwa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.