India-Coronavirus

Sabon nau'in Koronar India ya zarta wadanda suka gabace shi hatsari - WHO

Wasu ma'aikatan lafiya kula da lafiya a birnin New Delhi yayin kula da masu cutar Korona.
Wasu ma'aikatan lafiya kula da lafiya a birnin New Delhi yayin kula da masu cutar Korona. © Prakash Singh / AFP /Getty Images

Hukumar Lafiya ta duniya WHO ta ce akwai yiwuwar sabon nau’in cutar Korona da ya bulla a India ya fi na’uo’in cutar illa da kuma saurin yaduwa.

Talla

Cikin sabon binciken da ta gudanar kan sabon nau’in cutar da ke ci gaba da yaduwa a India, hukumar ta WHO ta ce nau’in cutar na B.1.617 da ya bulla cikin watan Oktoban bara yafi wadanda suka gabace shi hatsari.

Maria Van Kerkove wanda ya jagoranci tawagar ta WHO wajen gudanar da binciken, ta ce alamu sun nuna cutar ta Korona na sauyawa lokaci zuwa lokaci wanda ke sake nuna bukatar daukar tsauraran matakan tunkararta da kuma kare kai.

Wata mata yayin yi mata gwajin tantance kamuwa da cutar Korona a birnin Kolkata dake kasar India.
Wata mata yayin yi mata gwajin tantance kamuwa da cutar Korona a birnin Kolkata dake kasar India. © REUTERS/Rupak De Chowdhuri/Files

A jawabinta ga manema labarai, jami’ar ta ce nau’in cutar ta India babbar abar damuwa ce da kuma bukatar daukar matakan hadin kai daga bangarorin Duniya don kawar da ita.

India na ci gaba da ganin hauhawar cutar Korona tun bayan bullar sabon nau’in wanda ya kai ga samun mutune fiye da dubu 300 da ke kamuwa kowacce rana da kuma mutuwar kusan mutum dubu 4 a kullum.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI