China-Amurka-Falasdinawa

China ta zargi Amurka da yin biris da halin da Falasdinawa ke ciki

Shugaban China Xi JInping
Shugaban China Xi JInping © AFP

Kasar China ta zargi Amurka da zuba Ido game da yadda kasar Isra’ila ke barin wuta kan Falasdinawa, bayan da Amurkan ta dakatar da taron kwamitin tsaro na majalisar dinkin duniya da zai tattauna a game da shawo kan matsalar.

Talla

A cewar China fakewar da Amurka ta yi da rikicn Falasdinawa da yahudawa na hana taron kwamitin tsaro, ya nuna karara yadda take maraba da rikicin, kasancewar in har tana da sha’awar kawo karshen shi babu yadda za’a yi ta dage zaman kwamitin tsaro na majalisar dinkin duniya.

Ma’aikatar harkokin wajen China ta bakin jami’ar yada labaranta Hua Chunying ta shaida wa manema labarai cewa tun lokacin da rikicin ya barke China ke ta kira ga majalisar dinkin duniya da ta dauki matakin gaggawa kan rikicin Falasdinawan da Yahudawa.

Chinar ta ce alamu sun nuna karara, Amurka na da sha’awa kan rikicin Falasdinawan, la’akari da yadda ta nade hannayenta, amma da yake tana da wata bakar aniya kan china ta yi ta tada jijiyoyin wuya kan rikicin al’ummar Uighur.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.