Afghanistan - Taliban

Fada ya sake barkewa tsakanin dakarun Afganistan da Taliban

Mayakan Taliban a wajen birnin Lashkar Gah dake lardin Helmand yayin shirin afkawa mayakan Taliban a kasar Afghanistan.
Mayakan Taliban a wajen birnin Lashkar Gah dake lardin Helmand yayin shirin afkawa mayakan Taliban a kasar Afghanistan. © AFP/Sifatullahi Zahidi

Dakarun Afganistan sun cigaba da gwabza fada da mayakan Taliban a lardin Helmand dake kudancin kasar, abinda ya kawo karshen tsagaita wutar kwanaki uku da suka yi, domin baiwa jama’a  damar gudanar da bukukuwan Salla Karama cikin kwanciyar hankali.

Talla

Rahotanni sun ce an yi kazamar fafatawar tsakanin sojin na Afghanistan da Taliban ne a Lashkar Gha, babban birnin Lardin na Helmand, yankin da yayi kaurin suna wajen fuskantar hare-haren mayakan na Taliban, tun bayan da Amurka ta fara janye dakarunta daga kasar.

Zuwa wannan lokaci dai bayanai sun ce ana cigaba da gwabza fadan.

A ranar Juma’ar da ta gabata, wani harin bam da aka kai wani Masallaci ya halaka mutane 12 cikinsu har da limamin dake jagorantar Sallar Juma’a.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI