Falasdinawa - Isra'ila

Falasdinu ta caccaki kasashen Larabawan da suka maido da hulda da Isra'ila

 Ministan harkokin wajen Falasdinu, Riyad al-Maliki.
Ministan harkokin wajen Falasdinu, Riyad al-Maliki. Arif Yaman/Pool via Reuters

A Lahadin nan ministan harkokin wajen Falasdinu Riyad al-Maliki ya caccaki kasashen da suka maido da huldar diflomasiyya da Israila a shekarar da ta gabata, a daidai lokacin da tashin hankali ke dada kamari tsakanin Falasdinawa da Yahudawa.

Talla

Al-Maliki ya shaida wa wani taron gaggawa na kungiyar kasashen Musulmai ta duniya cewa maido da huldar diflomasiyya da Isra’ila ba tare da samun kwanciyar hankalin da ake bukata ba na alamta goyon baya ga cin zalin da Yahudawa ke yi.

Kasashen da suka maido da huldar diflomasiyya da Isra’ila dai su ne: Sudan, Morocco, Hadaddiyar Daular Larabawa da Bahrain.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.