China

Yanayin mai tsananin sanyi ya kashe masu gasar tsere sama da 20 a China

Masu aikin ceto a China, inda tsananin sanyi ya kashe masu gasar tsere.
Masu aikin ceto a China, inda tsananin sanyi ya kashe masu gasar tsere. AFP - STR

Mutane 21 sun mutu a China bayan da matsanancin yanayi na sanyi da iska da ruwan sama ya addabi wasu masu gasar tseren gudun –ya- da- kanin –wani na tsawon kilomita 100 a China, kamar yadda kafofin yada labaran kasar suka ruwaito a yau Lahadi.

Talla

Yanayin mai tsanani ya afka wa banagaren da aka gudanar da gasar tseren a yankin gandun dajin Yellow River Stone Forest kusa da birnin Baiyin a arewa maso yammacin lardin Gansu a tsakar ranar Asabar.

Magajin garin birnin Baiyin Zhang Xuchen  ya ce  da misalin tsakar ranar ne, ba tsammani wannan al’amari ya afka wa masu wannan gasa a daidai kilomita 20  zuwa 31.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.