Iran-Zabe

Iran ta fitar da sunayen 'yan takara 7 da za su fafata a zaben shugaban kasa

Shugaban Sashen Shari'ar Iran Ebrahim Raisi guda cikin 'yan takarar da za su fafata a zaben watan gobe.
Shugaban Sashen Shari'ar Iran Ebrahim Raisi guda cikin 'yan takarar da za su fafata a zaben watan gobe. ATTA KENARE AFP/File

Masu ra’ayin ‘yan mazan jiya, sun mamaye ‘yan takarar da za su fafata a babban zaben Iran na watan gobe, bayan da kasar ta fitar da sunan ‘yan takara 7 da za su fafata a wani yanayi da aka gaza ganin sunayen Mahmoud Ahmadinejad da Ali Larijani cikin jerin ‘yan takarar.

Talla

Cikin ‘yan takarar shugaban kasar da za su fafata a zaben na Iran karo na 13 da zai gudana ranar 18 ga watan gobe har da shugaban sashen shari’a Ebrahim Raisi wanda ya lashe kashi 38 na yawan kuri’un da aka kada a zaben 2017.

Zaben na zuwa a dai dai lokacin da Iran ke kokarin gyatta yarjejeniyar nukiliyarta ta 2015 tsakaninta da manyan kasashen Duniya, yayinda a bangare guda shugaba Hassan Rouhani ya rasa damar takara a karo na 3.

Jadawalin sunayen wanda Majalisar kolin addinin Musulunci ta Iran ta tantance kuma ma’aikatar cikin gida ta fitar, tun gabanin fitar sunayen ya gamu da caccaka sakamakon yadda ya fita ta bayan fage kuma cire sunayen wasu 'yan takara ya haddasa cece-kuce ciki har da tsohon shugaban kasa Mahmoud Ahmadinejad da kuma Ali Larijani.

Wannan ne karon farko da Majalisar kolin ta Iran ke gamuwa da kakkausar suka bayan fitar da sunayen 'yan takara hatta daga bangaren masu tsattsauran ra’ayi da ma masu sassaucin ra’ayi.

‘Yan takarar kamar yadda sanarwar ta nuna sun kunshi, shi kansa Ebrahim Raisi da Mohsen Rezai da Saeed Jalili sai Amirhossein Ghazizadeh Hashem da kuma Abdolnaseer Hemmati kana Mohsen Mehralizadeh da kuma Alireza Zakani.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI