Masar-Gaza

Masar ta fara gina Gaza da Isra'ila ta lalata

Wani bangare na Gaza da Isra'ila ta yi raga-raga da shi da rokoki
Wani bangare na Gaza da Isra'ila ta yi raga-raga da shi da rokoki AP - John Minchillo

Kasar Masar ta tura ayarin kayayyakin gine-gine da tawagogin injiniyoyi zuwa Gaza, domin shirin sake gina yankin Falasdinawa da Isra’ila ta yi wa ruwan bama-bamai a yakin baya-bayan nan da aka fafata da Hamas.

Talla

Hotunan bidiyon da kafar talabijin na gwamatin kasar suka watsa, sun nuna yadda motocin dakon kaya dauke da tutocin Masar suka isa kan iyakar kasar.

A ranar 20 ga watan Mayu, shugaban kasar Abdel Fatah Al Sisi ya yi alkawarin bayar da Dala miliyan 500 don taimakawa wajen sake gina Gaza, inda wasu Falasdinawa kimanin miliyan biyu ke rayuwa cikin matsin Isra’ila na kusan shekaru 15.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.