Lebanon - Faransa

Faransa na binciken rashawa kan shugaban babban bankin Lebanon

Lebanon's Central Bank chief Riad Salameh
Lebanon's Central Bank chief Riad Salameh © AFP/Dalati and Nohra

Faransa ta bude binciken kadarori da dukiyar shugaban Babban Bankin Lebanon Riad Salameh, wanda hukumomin kasar ke zargi da halasta kudaen haramun da kuma almunda hana.

Talla

Masu shigar da kara dake kula da harkokin kudade na birnin Paris sun bude bincike na farko game da batun aikata laifuka da halatta kudaden haram da ake zargin Salameh da aikatawa, kamar yadda wata majiya da ke kusa da binciken ta shaidawa kamfanin dillancin labarai na AFP,  bayan makamaicin matakin da kasar switzerland ta dauka.

Salameh dake rike da mukamin tun a shekarar 1993, ya sha zargi daga gwamnati da firaministan rikon kwarya Hassan Diab da cewa shi ke da alhakin durkusar da fam din Lebanon.

Jama’ar Lebanon na zargin shi da wasu manyan jami’ai da boye kudade a kasashen waje a yayin rikicin shekarar 2019, inda aka hanawa wasu daidaiku wannan dama.

Kuma tun daga wancan lokaci Labanon ta fada cikin matsalar tattalin arziki wanda Bankin Duniya ya bayyana shi, amatsayin mafi muni da aka taba gani tun cikin karni na 19.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.