Myanmar - Majalisar Dinkin Duniya

MDD ta nemi kasashen duniya su katse cinikin makamai da Myanmar

Sojojin kasar Myanmar yayin sintiri a lokacin da ake zanga-zangar adawa da gwamnatin sojojin da suka yi juyin mulki a birnin Yangon. 28/2/2021.
Sojojin kasar Myanmar yayin sintiri a lokacin da ake zanga-zangar adawa da gwamnatin sojojin da suka yi juyin mulki a birnin Yangon. 28/2/2021. © REUTERS/Stringer

Majalisar Dinkin Duniya ta bukaci ilahirin hukumomin kasashe da su bada hadin kai wajen dakile shigar makamai cikin kasar Myanmar, a cigaba da daukar matakin ladaftar da gwamnatin sojojin da ta yiwa tsohuwar shugaba Aung san Su Kyii juyin mulki a farkon watan fabarairun da ya gabata.

Talla

Kasashe 119 dake zauren majalisar dinkin duniyar ne suka amince da daukar matakin, 36 suka kaurace a yayin da Belarus ta hau kujerar naki.

A makon da ya gabata shugabar hukumar kula da ‘yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya Michelle Bachelet ta yi gargadin cewar tashe-tashen hankula na karuwa a sassan kasar Myanmar, tare da caccakar sojojin kasar da suka yi juyin mulki kan laifukan take hakkin dan adam da suke yi da sunan murkushe masu zanga-zangar adawa da su.

Cikin sanarwar da ta fitar Michelle Bachelete ta ce rahotannin da suka tattara sun nuna cewar rikici tsakanin kungiyoyin sa kai da jami’an tsaron Myanmar na cigaba da yin kamari a jihohin Kayah, Chin da Kachin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.