China - Coronavirus

'Yan kasar China biliyan 1 sun karbi allurar rigakafin korona

Wasu dake karbar allurar rigakafin annobar korona a arewacin kasar China, 12 ga watan Afrilu 2021.
Wasu dake karbar allurar rigakafin annobar korona a arewacin kasar China, 12 ga watan Afrilu 2021. AFP - STR

Kasar China ta sanar da cewa sama da mutum biliyan guda ne suka karbi allurar rigakafin cutar Covid-19 a kasar, yayin da kasar da ta fi yawan jama'a a duniya ta kara kaimin shirinta na rigakafin annobar. Sanarwar Hukumar Lafiya ta Kasar na zuwa ne bayan yawan  mutanen da suka harbu da cutar ya zarce biliyan biyu da miliyan 500 a duniya.

Talla

Hukumar lafiya ta kasar dai bata bayyana adadin mutanen da aka yiwa rigakafin kamar yadda tsarin yace ba, kasancewar yawancin alluran rigakafin da ake yi a kasar ta China ana yi ne sau biyu.

Hukumomi sun shirya yiwa kaso 40 cikin 100 na al’ummar kasar allurar mai dauke da yawan jama’a kusan biliyan daya da miliyan dari hudu daga nan zuwa karshen wannan watan.

Wasu lardunan suna ba da rigakafin kyauta don ƙarfafawa mutane. a wasu yankunan kuwa sai da aka bawa mutane dan tagomashi kafin ayi musu rigakafin

Sake barkewar annobar a baya-bayan nan a garin Guangzhou da ke kudancin kasar ita ma ta zaburar da hukumomin lafiya, musamman wuraren da suka gaza mayar da hankali sosai a kasar.

A ranar Lahadi, kasar ta China ta fitar da rahoton cewa mutum 23 aka gano sun harbu da cutar.

Ana sa ran China za ta samar da allurar rigakafin sama da biliyan uku a wannan shekarar, kamar yadda hukumomi a kasar suka ce.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI