Afghanistan-Taliban

Taliban ta yi ikirarin karbe kashi 85 na Afghanistan

Wasu mayakan Taliban.
Wasu mayakan Taliban. NOORULLAH SHIRZADA / AFP

Kungiyar Taliban ta yi ikirarin karbe  iko da kashi 85 na kasar Afghanistan, bayan da ta kwace mahimman iyakokin da suka hade kasar da kasashen Iran da Turkmenistan, biyo bayan munanan hare haren da ta kaddamar a kasar, a yayin da dakarun Amurka ke ida janyewa,  bayan kusan shekaru 20 a kasar.

Talla

Sa’o’i bayan da shugaban Amurka Joe Biden yak are ficewar dakarun kasar daga Afghanistan, kungiyar Taliban ta ce mayakanta sun kwace iyakoki masu mahimmanci a yammacin Afghanistan, lamarin da ya fadada yankunan da ke hannunta zuwa iyakokin kasar da Iran da China.

A yayin wata ziyara a birnin Moscow, wata tawagar jami’an Taliban ta ce gundumomi 250 daga cikin 398 na Afghanistan na karkashin ikonta, ikirarin da ke da matukar wahalar tantancewa ko karyatawa ga gwamnatin kasar.

 A waje daya kuma, kakakin Taliban, Zabihullah Mujahid ya shaida wa kamfanin dillancin labaran Faransa cewa mayakansu sun karbe garuruwan Islam Qala, da ke iyaka da Iran, da Torghundi na iyaka da Turkmenistan.

Ma’aikatar cikin gidan Afghanistan, ta bakin kakakinta, Tareq Arian ta ce ana nan ana shirye-shiryen kawar da ‘yan ta’adda daga wuraren da suka kwata.

Bayan kusan shekaru 20, shugaban Amurka Joe Biden ya ce aikin da dakarun kasar ke yi a Afghanistan zai zo karshe a ranar 31 ga watan Agusta, sai dai ya bayyana shakkun ko hukumomin kasar za su iya jan ragamar kasar gaba daya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.