Afghanistan - Taliban

An tsaurara matakan tsaro a Kabul saboda shirin Taliban na kwace birnin

Jami'an tsaron Afghanistan wajen wani asibiti dake birnin Kaboul da aka kaiwa hari 12 ga watan Mayu 2020. REUTERS/Mohammad Ismail/File Photo
Jami'an tsaron Afghanistan wajen wani asibiti dake birnin Kaboul da aka kaiwa hari 12 ga watan Mayu 2020. REUTERS/Mohammad Ismail/File Photo REUTERS - MOHAMMAD ISMAIL

Hukumom a Afghanistan sun karfafa matakan tsaro a birnin Kabul fadar gwamnatin kasar, lura da yadda mayakan Taliban ke ci gaba da kwace muhimman yankuna daga hannun dakarun gwamnati, sannan kuma ake fargabar cewa za su iya kwace birnin. Tuni dai wasu kasashe suka fara kwashe al’ummominsu daga kasar saboda fargabar abin da zai iya furuwa.

Talla

Yayin da Amurka da kawayenta ke cewa za su kammala aikin janye dakarunsu daga kasar ta Afghanistan kafin ranar 31 ga watan gobe na agusta, a nasu bangaren mayakan Taliban sun tsananta kai hare-hare kan dakarun gwamnati tare da kwace ikon yankunan da aka bayyana cewa sun kai 85% na fadin kasar daga hannun dakarun gwamnatin kasar.

Tuni dai wuraren binciken jami’an tsaro da ke kan iyakokin kasar da Tajikistan suka fada hannun dakarun kungiyar ta Taliban, kamar dai yadda aka samu faruwar hakan a wasu wuraren binciken jami’an tsaro da ke iyaka da Iran.

Mai magana da yawun ma’aikatar cikin gidan kasar Tariq Arian, ya ce an girke manyan makamai a kusa da filin sauka da tashin jiragen saman birnin Kabul, duk da cewa Turkiyya ta yi alkawarin kare shi bayan janyewar dakarun Amurka da kungiyar tsaro ta Nato da ke taimaka wa takwarorinsu na Afghanistan daga sama,

Lamarin dai yana da ban tsoro matuka, domin ko baya ga kasashen Yamma da suka fara janye wasu daga cikin jami’ansu na diflomasiyya daga Kabul, ita ma India ta janye jami’anta daga karamin ofishin jakadancinta da ke Kandahar birnin mafi girma a kudancin kasar da ke matsayin cibiyar ‘yan Taliban.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.