India - Ambaliya

Zaftarewar kasa ta hallaka sama da mutane 76 a India

Yankin kasar India da ya fuskanci Ambaliyar ruwa a yammacin kasar, 23, 07,21
Yankin kasar India da ya fuskanci Ambaliyar ruwa a yammacin kasar, 23, 07,21 - INDIAN NAVY/AFP

Adadin wadanda suka rasa rayukansu a zaftarewar Laka a India ya kai 76, yayin da Masu aikin ceto ke aikin laluben masu sauran numfashi.

Talla

Ta farko Jami’ai suka ce akwai kimanin muatne 68 da suka bata bayan ruwan sama kamar da bakin kwarya da ya afkawa gabar tekun yammacin Indiya, lamarin da ya haifar da zaftarewar kasa da ta binne gidaje da dama a gundumar Raigad dake kudancin Mumbai.

Kokarin Sojojin Ruwa da na Sama na kwashe mutanen da ambaliyar ta rutsa da su, ya gamu da cikas, sakamakon toshewar hanyoyi, ciki harda babbar titi tsakanin Mumbai da Goa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI