India - Ambaliya

Adadin wadanda zaftarewar kasa ta kashe a India ya zarta 127

Masu aikin ceto a kasar India na kokarin lalubo masu sauran nunfashi, bayan zaftarewar kasa da ta hallaka mutane 126, 18 -07-21.
Masu aikin ceto a kasar India na kokarin lalubo masu sauran nunfashi, bayan zaftarewar kasa da ta hallaka mutane 126, 18 -07-21. REUTERS - NIHARIKA KULKARNI

Adadin wadanda suka mutu sakamakon ambaliyar ruwa da zaftarewar kasa a Indiya ya haura zuwa 127 a ranar Lahadi, yayin da masu aikin ceto ke neman wasu da dama da suka bata.

Talla

Yankin yammacin kasar dake gabar teku ya fusknaci  ambaliyar ruwa tun ranar Alhamis, sakamakon ruwan sama kamar da bakin kwarya da aka shatata, yayin da hukumar kula da Yanayi na Indiya da ke gargadin yiwuwar sake saukar ruwan sama a 'yan kwanaki masu zuwa.

Ambaliyar ruwa da zaizayar kasa na zama ruwan dare India lokutan damina, wanda kuma galibi yakan rusa gine-gine mara inganci duk lokacin da aka samu ruwan sama babu kakkautawa.

Masana sun ce canjin yanayi ya haifar da ambaliyar shekara-shekara ta karu a mita da kuma karfi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.