Afghanistan-Taliban

Hare-haren Taliban: An sanya dokar hana yawon dare a Afghanistan

Dakarun Afghanistan a yayin gwabzawa da 'yan Taliban a shekarar 2015. Yan kungiyar Taliban na samun galaba, biyo bayan janyewar dakarun Amurka.
Dakarun Afghanistan a yayin gwabzawa da 'yan Taliban a shekarar 2015. Yan kungiyar Taliban na samun galaba, biyo bayan janyewar dakarun Amurka. Wakil KOHSAR AFP/File

Hukumomin  Afghanistan sun sanya dokar hana yawon dare a larduna 31 cikin 34 na kasar don shawo kan dirar mikiyar da kungiyar Taliban ta kaddamar a kasar a cikin kwanakin nan, a cewa ma’aikatar cikin gidan kasar.

Talla

 Hare-haren da kungiyar Taliban ta kaddamar a fadin kasar sun sa ta karbe iko da mahimman iyakoki, gwamman gundumomi da manyan biranen larduna, kana ta yi wa wasu manyan birane kawanya, tun a farkon watan Mayu da dakarun kasashen waje karkashin jagorancin Amurka suka fara janyewa daga kasar.

A wata sanarwa, ma’aikatar ta ce dokar hana yawon daren da za ta fara aiki tsakanin karfe 10 na dare zuwa 4 na asuba za ta shafi dukkan larduna, amma ban da biranen Kabul, Panjshir da Nangarhar.

Sakamakon janyewar dakarun Amurka da na kasashen waje a Afghanistan, kungiyar Taliban ta karbe iko da gundumomi kimanin 400.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.