Hong Kong

An daure wani matashi shekaru 9 saboda cin amanar kasa

Jami'an tsaron Hong Kong
Jami'an tsaron Hong Kong Isaac Lawrence AFP

Wata Kotu a Hong Kong ta yanke wa wani mai hidimar raba abinci a shagon sayar da abinci, hukuncin shekaru 9 a gidan yari bisa samun sa da laifin cin amanar kasa da kuma take wasu dokoki da aka shimfida.

Talla

Tun da fari, jami’an tsaro sun cafke Tong Ying-kit mai shekaru 24 a ranar Talatar da ta gabata sakamakon kama shi da laifin afka wa wasu jami’an ‘yan sanda guda uku, lokacin da suke bakin aiki.

Baya ga wannan laifin, an kuma kama Tong da laifin daga tutar da ke nuna alamun zanga-zanga, kwana guda bayan da jami’an tsaro suka hana gudanar da kazamar zanga-zangar da ta gudana a ranar 1 ga watan Yuli.

Wannan dai ya zama izina tare da bude wani sabon shafin yanke hukunci mai tsanani kan masu take doka a yankin na Hong Kong, baya ga masu tada rikicin siyasa.

An dai yanke wa mutumin hukuncin ne ba tare da sauraren shedu ba, yayin da alkalai ukun da suka saurari karar suka amince da hukuncin da aka yanke masa.

A cewar alkalan, wanda ake zargin ya aikata laifin ta’addanci, tare kuma da yunkurin tayar da wani sabon rikici a yankin dalilin daga tutar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.