Afghanistan-Ta'addanci

Dan sanda ya mutu a harin da aka kai Majalisar Dinkin Duniya a Afghanistan

The Taliban have stepped up their operations across Afghanistan as foreign forces wrap up their withdrawal
The Taliban have stepped up their operations across Afghanistan as foreign forces wrap up their withdrawal WAKIL KOHSAR AFP/File

Wani dan sandan Afghanistan ya mutu yayin wani hari da aka kai harabar ginin majalisar dinkin duniya a birnn Herat, a yayin da ake ci gaba da baiwa hammata iska tsakanin mayakan Taliban da dakarun gwamnati a wajen birnin da ke yammacin kasar.

Talla

Rikici ya ta’azzara a kasar ne a farkon watan Mayu, lokacin da kungiyar Taliban ta kaddamar da munanan hare hare a sakamakon karkare janyewar sojojin kasashen waje dake karkashin jagorancin Amukra daga kasar.

Mayakan Taliban din sun karbe iko da gundumomi da dama a kasar, ciki har da lardin Herat, inda suka kuma kwace iyakoki biyu da suka hade Iran da Turkmenistan.

A jiya Juma’a, ‘yan Taliban din sun gwabza fada da dakarun gwamnati a wajen birnin na Herat, lamarin da ya tilasta wa iyalai da dama  arcewa daga gidajensu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.