Korea ta Arewa-Amurka

Korea ta Arewa ta yi gwajin sabon makami da ke cin dogon zango

Sabon makamin da Korea ta Arewa ta yi gwaji a karshen mako.
Sabon makamin da Korea ta Arewa ta yi gwaji a karshen mako. STR KCNA VIA KNS/AFP

Wasu rahotanni daga Korea ta Arewa sun ce kasar ta yi gwajin wani makami mai linzami da ke cin dogon zango a ranakun karshen mako, gwajin da tuni ya gamu da sukar Amurka bayan da ta bayyana shi a matsayin barazana ga makwabtan Korean da ma kasashen gefe.

Talla

Hotunan gwajin makamin wanda jaridar Rodong Sinmun ta wallafa ya nuna yadda makamin ya fita daga turke daya cikin turaku biyar da ke dashe a wajen gwajin cikin tsananin gudu zuwa sararin samaniya.

Wani masanin makamai da ke sharhi kan sabon gwajin na Korea ta Arewa, ya ce gwajin makamin nan una yadda kasar ta kara karfafa sashenta na fasahar samar da muggan makamai.

Amurka dai ta nanata kargadi kan yadda Korea ke makwabtaka da aminanta da suka kunshi Korea ta kudu da Japan kan ci gaba da fadada bangaren makaman nata wanda ta ce barazana ce ga tsaronsu.

Kamfanin dillancin labaran Korea na KCNA ya ruwaito cewa gwajin ya gudana ne a ranakun asabar da lahadi wanda ke bayyana cewa gwajin makamin ya yi nasara kamar yadda aka tsara.

Acewar kamfanin sabon makamin na tafiyar kilomita dubu 1 da 500 dai dai da mil 930 ko kuma tsawon sa’o’I biyu a sararin samaniya kafin sauka, dauke da sassa 8 wanda ke nuna yana da karfinn iya tsallake fadin kasar Korea ta Arewan da ruwanta baki daya zuwa yankin da aka nuface shi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI