Majalisar Dinkin Duniya-Afghanistan

Dole kasashen duniya su yi mu'ammala da Taliban don ceto Afghanistan - Guterres

Antonio Guterres, sakataren Majalisar dinkin duniya.
Antonio Guterres, sakataren Majalisar dinkin duniya. Kenzo TRIBOUILLARD POOL/AFP/File

Sakatare janar na majalisar dinkin duniya Antonio Guterres ya ce ya zama wajibi manyan kasashen duniya su mu’amalanci Taliban don gujewa rugujewa Afghanistan baki daya.

Talla

Antonio Guterres ya ce akwai bukatar manyan hukumomin duniya da kasashe su mu’amalanci Taliban kasancewar hadari ne kaurace mata, wanda kuma zai iya kai wa ga karasa ruguza kasar baki daya.

Guterres na wadannan kalamai ne ga manema labarai, jim kadan bayan kammala taro kan wata gidauniya da aka kaddamar da nufin taimaka wa jama’ar Afghanistan.

A cewar sa sanya idanun kasashe duniya da kuma yin mu’amala da gwamnatin Taliban ne kadai zai ceto jama’ar kasar daga matsanacin talauci da yunwa da kuma kare su daga cin zarafin dan adam.

Taron da aka gudanar ranar Litinin, na da nufin samar da wata gidauniya da za’a tara akalla dala miliyan dari 6 don tallafa wa jama’ar Afghanistan da yanzu haka ke fuskatar matsanacin talauci da tsananin yunwa sakamakon tsayawar al’amurra cik, tun bayan da Taliban ta karbe iko da gwamnatin kasar.

Tun a tsakiyar watan Agusta lokacin da Taliban ta karbe iko da mulkin Afghanistan ne kasashe suka fara yanke hulda da Afghanistan da kuma cin alwashin kauracewa duk wata mu’amala da ita, abin da Guterres ke ganin cewa gurgiuwar shawara ce.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.