Taliban-Afghanistan

Taliban ta gargadi manyan kasashe kan sanyawa Afghanistan takunkumi

Gwamnatin Taliban a Afghanistan ta gargadi kasashen Turai da Amurka game da matakan da su ke dauka na sanya mata takunkuman karya tattalin arziki wanda kungiyar ke cewa zai kara matsalar tsaro baya ga kara yawan ‘yan ciranin da za su kwararu kasashen nasu.

Ministan harkokin wajen Afghanistan Amir Khan Muttaqi.
Ministan harkokin wajen Afghanistan Amir Khan Muttaqi. Hoshang Hashimi AFP/File
Talla

Ministan harkokin wajen Afghanistan Amir Khan Muttaqi ya shaidawa wakilan kasashen yammacin Duniyar a tattaunawarsu a Doha cewa gurgunta gwamnatin Taliban ba kadai kasar zai illata ba, domin kuwa zai kara matsalar tsaron da Duniya ke fuskanta baya ga karuwar ‘yan ciranin da ke tururuwa zuwa manyan kasashe.

A watan Agustan da ya gabata ne, Taliban ta hambarar da gwamnatin Ashraf Ghani mai samun goyon bayan Amurka wanda ya kawo karshen rikicin shekaru 20 da Afghanistan ta yi fama da shi baya ga mayar da kasar turbar mulkin gargajiya bisa tsarin addinin Islama, sai dai matsalolin rashin kudin shiga sun dabaibaye kasar ta yankin Asiya musamman bayan kullemata asusun ajiyar da manyan kasashen suka yi da kuma katse tallafin da ta ke samu.

Ka zalika kokarin Taliban na dawo da zaman lafiya a kasar na fuskantar babbar barazana daga mayakan IS baya ga matsalar tattalin arziki da ke ci gaba da tsananta sakamakon takunkuman manyan kasashen Duniya akan kasar wanda ya haddasa karanci kudi a ilahirin bankunan Afghanistan.

Acewar ministan wajen na Afghanistan ta bakin kakakinsa, yayin zantawar ta su ta Doha matukar kasashen duniyar na bukatar zaman lafiyarsu, akwai bukatar su kawo karshen takunkuman kan Afghanistan wanda zai bata damar tafiyar da harkokinta musamman al’amuran da suka shafi tattalin arziki.

Muttaqi ya roki kassahen su bai wa Afghanistan damar tafiyar da harkokin kudi a bankuna baya ga sahale ayyukan agaji don ceto kasar daga durkushewa.

Turai dai na da fargabar karuwar kwararuwar ‘yan cirani idan har tattalin arzikin Afghanistan ya rushe wanda ya sa ta ke shirin matsa kaimi ga makwabtanta da suka kunshi Pakistan da Iran don su tsaurara matakn tsaro a iyakokinsu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI