Nukiliya-Korea ta Arewa

Korea ta Arewa ta sake gwajin shu'umin makamai karo na 2 a mako guda

Karo na biyu kenan cikin kasa da mako guda da Korea ta Arewa ta aiwatar da makamancin gwajin.
Karo na biyu kenan cikin kasa da mako guda da Korea ta Arewa ta aiwatar da makamancin gwajin. via REUTERS - KCNA

Korea ta Arewa ta sake gwajin wani shu’umin makami mai linzami da ta harba cikin teku a yau talata, gwajin da ke matsayin irinsa na biyu cikin kasa da mako guda, dai dai lokacin da makwabciyarta Korea ta kudu ke gargadi kan yadda sashen nukiliyar abokiyar gabarta ta ke sake bunkasa.

Talla

Da safiyar yau ne Pyongyang ta aiwatar da gwajin wanda ta bayyana da hypersonic wato nau’in shu’umin makamin da ke da matukar gudu kwatankwacin ninkin saurin sauti sau 5 ko kuma gudun kilomita dubu 6 da 200 cikin sa’a guda dai dai mil daya a duk dakika daya ko da ya ke fadar gwamnatin Korea ta kudu ta bayyana shakku kan ko nau’in makamin ya kai yadda makwabciyartata ke ikirari.

Sai dai ma’aikatar tsaron Korea ta Kudun ta bayyana cewa yanayin gwajin makamin na yau gudu da kuma karfinsa ya zarta wanda kasar ta yi a makon jiya, alamun da ke nuna ta sake samun gagarumin ci gaba a kankanin lokaci.

A wannan karon shu’umin makamin na Korea ta Arewa ya isa gab da da’irar kasuwancin Japan duk da cewa babu bayanin wata barna da yayi, sai dai tuni Firaminista Fumio Kishida ya yi tir da gwajin tare da bayyana shi a matsayin yunkurin takalar fada.  

Gwajin shu’umin makamin na Korea ta arewa na zuwa ne dai dai lokacin da kwamitin tsaro na Majalisar Dinkin Duniya ke shirin zaman a musamman kan gwajin farko da kasar ta yi kasa da mako guda.

Tun bayan hawan Kim Jong Un mulki, Korea ta Arewa ke karfafa sashen makaminta kuma matukar ya tabbata gwajin na ta na yau na jerin Hypersonic Missile kenan kasar ta shiga sahun kasashen Amurka Rasha da kuma China da ke da irin makamin.

Nau’in makamin na jerin shu’uman makamai masu linzami da kawo yanzu babu na’urorin taresu ko kuma lalata su gabanin isa inda aka aikesu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI