Girka

Mutane 3 Sun Mutu Yau

Masu Bore da 'yan sanda
Masu Bore da 'yan sanda rfi

Rahotanni daga kasar Girka na cewa akalla mutun uku ne suka mutu yau sakamakon wani harin bam da aka kai wani Banki a tsakiyar birnin Athens, yayin da aka kwashe mutane 20 daga cikin ginin.Wannan bam, an tasar dashi ne a lokacinda masu bore saboda matakan tsuke bakin aljihu ke cigaba da yi afadin kasar.Bayanai na nuna cewa ‘yan sanda sunyi ta fesa hayaki mai sa hawaye domin tarwatsa masu boren.Bayaga boren na Athens, bayanai na nuna anyi wani bore a birnin Thessalonoki.Mutane masu tarin yawa ne dai suka shiga boren na yau afadin kasar ta Girka, wanda kungiyoyin kodago suka nemi ayi saboda nuna rashin gamsuwar su da matakan tsuke bakin aljihu, da niyyar kuntatawa talaka.Wannan bore, na gamagari na kwanaki biyu a jere, shine karo na uku tun lokacinda kasar ta fuskanci matsalar komadan tattalin arzikin nata.Harkokin sufuri dana yau da kullum sun tsaya cik afadin kasar.