India

Mutane 8 Sun Rayu A Hatsari Jirgin Sama

Destroços do avião da Air India Express em Mangalore.
Destroços do avião da Air India Express em Mangalore. rfi

An samu mutane takwas da sauran nunfashi daga cikin mutane samada 160 dake cikin jirgin saman fasinja daya fadi akasar Indiya.Da fari ance babu daya daga cikin fasinjojin daya sami tsira saboda yadda harabar da jirgin ya fadi, ya turnuke da hayaki da wuta.Hatsarin ya auku ne a filin jiragen sama na garin Mangalore, dake Jihar Karnataka.Wasu kafofin da fari na cewa akwai akalla mutane 4 dake da sauran nunfashi.Wani Mukaddashin ‘Yan sandan yankin Ramesh yace zaiyi wuya asami wani da sauran nunfashi.Wannan jirgin sama dai ya taso ne daga Dubai kuma mallakin kamfanin jiragen Sama na Air India Express ne.Jirgin kirar Boeing 737-800 na dauke da mutane 166 ne cikinsu maaikata 6.Bayanai na nuna cewa jirgin ya kasa tsayawa ne alokacin da yake sauka, kafin yayi bindiga ya kama da wuta.Daga cikin wadan da suke nunfashi har akwai wata ‘yar karamar yarinya, wadda masu aikin agaji suka tsamo.Bayanan na nuna cewa dukkan fasinjojin ‘yan asalin kasar Indiya ne.