Isa ga babban shafi
Pakistan

Yan bindiga sun kashe mutane 80 a Masallatai biyu

Hari cikin Masallatan kasar Pakistan 28 mai.
Hari cikin Masallatan kasar Pakistan 28 mai. Reuters/Mani Rana
Zubin rubutu: Suleiman Babayo

Wasu 'yan bindiga, a kasar Pakistan, sanye da kyallen da ya rufe musu fuska, sun kashe mutane 80 a Massalatai biyu na birnin Lahore.Rahotanni sun ce, Yan bindigan dauke da makamai da gurneti, sun yiwa Massalatan tsinke, inda suka tada bama bamai, kuma suka yi ta harbi, abinda ya kaiga rasa rayukan mutane da dama.Massalatan biyu dai mallakam mabiya darikar Ahmadiya ne, wanda hukumomin Pakistan suka baiyana su a matsayin wadanda ba Musulmai ba.Ana dai zargin masu tsatsauran ra’ayi ne da kai wannan hari, wanda ya dada fito da tashin hankalin da ake fama da shi a cikin wannan kasa.Akalla mutane 3,370 irin wadanna Yan bindigan suka kashe a cikin shekaru uku.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.