Izira'ila-Palesdinawa

Mutane 10 sun hallaka sakamakon farmakin Izira'ila

رویترز

Akalla mutane 10 aka kashe, yayin da sojin ruwan Israela, suka kutsa kai, cikin jiragen dake dauke da kayan agaji zuwa Yankin Gaza na Palesdinawa.Wani gidan talabijin mai zaman kansa a Israela, ya ce sojin sun bude wuta kan masu dauke da kayan agajin, inda suka kashe mutane goma, kuma wasu da dama sun samu raunuka.Tuni Kasar Turkiya, ta gaiyaci jakadan Israela a kasar, dan baiyana rashin jin dadin ta, kan harin da aka kai kan jirgin ta. Kungiyar kasashen Tarayyar Turai ta yi kirar kafa kwamitin bincike, domin gano gaskiyar abunda ya faru.Jiragen ruwan suna dauke da kayayyakin abinci tonnes dubu 10, na agaji da aka dauko daga tashar ruwan Cyprus ranar Lahadi, kuma ake saran ya isa yankin Gaza na Palesdinawa ranar Litinin.