Isra'ila

Isra’ila ta fara korar wadanda ta kama a harin jiragen agaji

KASAR Isra’ila yau ta fara maida mutanen da ta tsare, bayan harin jiragen ruwan dake dauke da kayan agaji zuwa Yankin Gaza.Rahotanni sun ce, yanzu haka an tasa keyar mutane 250 da aka tsare zuwa kasashensu, kuma 120 sun fitone daga kasashen Algeria da Indonesia, yayin da 60 kuma suka fito daga Turkiya.Kasar Faransa, tace akwai Yan kasar ta tara, da ba’aji duriyarsu ba, a dai dai lokacin da Sakataren harkokin wajen Britaniya, William Haque ke cewa, Yan kasar sama da 40 ke cikin tawagar.Sakamakon korafin kasashen duniya kan lamarin, kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya, ya bukaci gudanar da bincike na hakika, kan lamarin.Rahotanni sun ce, Isra’ila ta fara kwashe iyalan jami’an diplomasiyar ta dake Turkiya, ganin abinda matsalar ta haifar.Kasar Nicaragua, yau ta sanar da katse huldar jakadanci da Israela, dangane da lamarin. 

Expulsés par les autorités israéliennes, des ressortissants turcs posent pour les médias à leur arrivée à l'aéroport d'Ataturk, à Istanbul.
Expulsés par les autorités israéliennes, des ressortissants turcs posent pour les médias à leur arrivée à l'aéroport d'Ataturk, à Istanbul. Bulent Kilic/AFP