Afghanistan

An kaddamar da taron magance tashin hankalin Afghanistan

Omar Sobhani/Reuters

YAU an kaddamar da wani taron shugabanin Yankunan kasar Afghanistan, dan samo bakin zaren warware matsalar tashin hankalin da aka kwashe shekaru tara anayi a cikin kasar.Taron wanda ya samu halartar shugabani 1,600, shine irinsa na uku, a kokarin da shugaba Hameed Karzai keyi, na hada kan Yan kasar, kuma yana samun goyan bayan jami’an tsaro 12,000.Taron na samun wakilcin mata 300, wanda shine kashi 20 na masu halartar sa.