Japan

Pri Ministan Japan yayi murabus

PRI Ministan Kasar Japan, Yukio Hatoyama
PRI Ministan Kasar Japan, Yukio Hatoyama

PRI Ministan Kasar Japan, Yukio Hatoyama, ya sauka daga mukamin sa, watanni takwas bayan karbar ragamar tafi da kasar.Murabus din Hatoyama, ya biyo bayan karya alkawarin da ya yiwa Yan kasar, na cewa idan yah au karagar mulki, zai dauke sansanin dakarun Amurka dake kudancin Tsibirin Okinawa, alkawarin da ya karya a watan jiya.Sakamakon karyar alkawarin Jam’iyar da ke kawance da ta Hatoyama, ta janye daga Gwamnati, abinda ya janyo matsin lamba cewar, ya sauka daga mukaminsa.