Thailand

Pri Ministan Thailand ya tsallake rijiya da baya

PRI Ministan kasar Thailand, Abhisit Vejjajiva,
PRI Ministan kasar Thailand, Abhisit Vejjajiva, REUTERS/Chaiwat Subprasom

PRI Ministan kasar Thailand, Abhisit Vejjajiva, ya tsallake rijiya da baya, bayan kada kuri’ar rashin amincewa da Gwamnatin sa, sakamakon yadda ya umurci soji anfani da karfin da ya wuce kima, kan masu zanga zanga.Masu adawa da Pri Ministan, sun zarge shi da cin zarafin Bil Adama, saboda yadda soji sukayi anfani da harsasai wajen murkushe masu zanga zangar, abinda ya kaiga mutuwar mutane 89, kana kuma kusan 2,000 suka samu raunuka.Yan Majalisu 186 suka kada kuri’ar Allah wadai da Gwamnatin, yayin da 246 suka ki, kamar yadda Kakakin Majalisar, Chai Chidchob ya bayyana.